Home Labarai Da ɗumi-ɗumi: Nasiru Gawuna ya sauka daga shugabancin FMBN

Da ɗumi-ɗumi: Nasiru Gawuna ya sauka daga shugabancin FMBN

0

Shugaban hukumar gudanarwar bankin bada lamunin gidaje na Najeriya watau Federal Mortgage Bank of Nigeria FMBN, Nasiru Yusuf Gawuna, kuma ɗan takarar Gwamnan Kano a zaɓen da ya gabata na shekarar 2023, ya yi murabus daga mukaminsa, matakin da zai fara aiki nan ta ke.

Jaridar BizPoint ta ruwaito cewa, rahotanni sun nuna Gawuna ya kammala shirin sauya sheƙa zuwa jam’iyyar ADC tare da tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, kuma ana sa ran zai sanar da hakan a hukumance a ranar Talata.

A cikin wasiƙar murabus da ya rubuta ranar 27 ga watan nan da muke ciki na Maris, ya bayyana cewa, matakin ya yi dai-dai da umarnin Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, wanda ya bukaci dukkan masu muƙaman siyasa su sauka domin bin dokokin zaɓe gabanin harkokin siyasa masu zuwa.

Gawuna ya nuna godiya ga shugaba Tinubu bisa damar da aka ba shi na yi wa ƙasa hidima, yana mai cewa lokacinsa a FMBN ya ba shi damar ba da gudummawa wajen bunƙasa bankin da kuma ƙasar baki ɗaya.
Ya jaddada cewa murabus ɗinsa ya biyo bayan bin ƙa’idojin dokar zaɓe wadda ta yi tanadin cewa masu riƙe da muƙaman siyasa su sauka kafin shiga harkokin siyasa, domin tabbatar da gaskiya da adalci a tsarin zaɓe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here