Tsohon mataimakin gwamnan Kano, Alhaji Nasiru Yusuf Gawuna, ya koma jam’iyyar ADC a hukumance, inda ya kammala rajista tare da karɓar katin zama ɗan jam’iyya a mazabarsa ta Gawuna da ke ƙaramar hukumar Nasarawa a jihar.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa Nasiru Gawuna ya je yin rajistar tare da jagoran tafiyar Kwankwasiyya kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP a zaɓen 2023, Rabiu Musa Kwankwaso, wanda shi ma ya yi rajista a matsayin ɗan jam’iyyar ADC a yau Litinin.
Komawar tasa dai, ta biyo bayan sanarwar da Gawuna ya yi ta ficewa daga jam’iyyar APC a daren jiya Litinin, lamarin da ke nuna sauyi mai muhimmanci a tafiyarsa ta siyasa.
A yayin rajistar, magoya baya da manyan jiga-jigan jam’iyya sun hallara domin shaida wannan lamari tare da nuna goyon bayansu ga tsohon ɗan takarar gwamna na APC a zaɓen 2023.
Taron ya kasance mai cike da jama’a, inda aka ga yadda magoya baya suka fito domin nuna farin ciki da goyon baya ga sabon matakin da Gawuna ya ɗauka.








