Home Muhalli NiMET ta yi hasashen samun rana da ƙura na tsawon kwanaki 3

NiMET ta yi hasashen samun rana da ƙura na tsawon kwanaki 3

0

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya NiMet, ta yi hasashen samun yanayin rana tare da ƙura a sassan ƙasar daga yau Lahadi zuwa Talata mako mai kamawa.

Hukumar ta bayyana haka ne ta cikin wani rahoto ta fitar a Asabar din nan a birnin tarayya Abuja.

NiMet ta kuma bayyana cewa, yankin Arewa zai fuskanci yanayin hasken rana a duk tsawon lokacin, yayin da ake sa ran yanayin ƙura a jihohin Arewa ta Tsakiya.

Hukumar ta kuma sanar cewa a safiyar ranar Lahadi za a samu tsawa tare da ruwan sama kaɗan a wasu sassan jihohin Ribas, Bayelsa da Delta.

Daga baya a ranar Lahadi, ana sa ran samun tsawa a wurare daban-daban na jihohin Ribas, Delta, Cross River, Akwa Ibom da Bayelsa.

A ranar Litinin, NiMet ta yi hasashen ci gaba da samun rana a Arewa da kuma yanayin ƙura a Arewa ta Tsakiya, yayin da jihohin Kudu za su fuskanci gajimare da safe sannan tsawa a wasu wurare daga baya a rana.

A ranar Talata, hukumar ta bayyana cewa yanayin rana da ƙura zai ci gaba a Arewa da Arewa ta Tsakiya, yayin da a Kudu za a samu gajimare da safe sannan tsawa tare da ruwan sama matsakaici daga baya.

NiMEat, ta bada shawarwarin ɗaukar matakan kariya ga masu fama da cututtukan numfashi da kuma gargadin direbobi da kamfanonin jiragen sama su bi rahotannin yanayi na NiMet.

Solacebase

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here