Home Siyasa Ƴan majalisar wakilai 8 daga Kano sun koma APC daga NNPP

Ƴan majalisar wakilai 8 daga Kano sun koma APC daga NNPP

0

Ƴan Majalisar Wakilai takwas na Kano, sun fice daga jam’iyyar NNPP tare da komawa jam’iyyar APC, lamarin da ya ƙara girgiza siyasar jihar.

Shugaban Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, ne ya sanar da sauya sheƙar a hukumance yayin zaman majalisar a yau Talata, bayan karanta wasiƙun da ‘yan majalisar suka aike wa zauren.

A cikin wasiƙun nasu daban-daban, ‘yan majalisar sun bayyana cewa rikice-rikicen cikin gida da ke addabar jam’iyyar NNPP ne ya tilasta musu ɗaukar wannan mataki.

Wannan sauyin ya samu halartar Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf, da Mataimakin shugaban majalisar Dattawa Barau Jibrin, da tsohon Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, da sauran manyan ‘yan siyasa.

‘Yan majalisar da suka sauya sheƙar sun haɗa da Tijjani Abdulkadir Jobe (Dawakin Tofa/Rimin Gado/Tofa), Garba Ibrahim Diso (Gwale), Hassan Shehu Hussain (Nassarawa), Idris Dankawu (Kumbotso), Muhamamad Chiroma Nalaraba (Gezawa/Gabasawa), Barr. Rabiu Yusuf (Takai/Sumaila), Dr. Ghali Mustapha Tijjani (Albasu/Gaya/Ajingi) da Barr. Muhammad Bello Shehu (Fagge).

Solacebase

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here