Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya koma jam’iyyar APC a yau Litinin.
Gwamnan, ya sanar da batun komawa jam’iyyar tasa ta baya ne yayin wani taro da aka gudanar a ɗakin taro na Coronation da ke fadar gwamnatin Kano, inda ya bayyana cewa ya ɗauki matakin ne bisa la’akari da muradun al’ummar jihar.
Haka kuma, Gwamna Abba Kabir, ya jaddada cewa, ya yi kome cikin jam’iyyar APC domin ƙarfafa haɗin kai, kwanciyar hankali da kuma ci gaban jihar Kano, tare da tabbatar da cewa bayar da kyakkyawan shugabanci da amfanin dimokuraɗiyya ga al’umma ne babban fifikonsa.








