Allah ya yi wa mai magana da yawun Hukumar kashe gobara ta Jihar Kano Saminu Yusuf Abdullahi rasuwa.
Jaridar SolaceBase ta ruwaito cewa shugaban sashen hukumar ta kashe gobara na ƙaramar hukumar Dambatta, PFS2 Muhammad Ibrahim Nasiru, ne ya tabbatar da rasuwar tasa ga manema labarai a yau Laraba.
Ya ce, An gudanar da jana’izarsa da misalin ƙarfe 8:30 na safiyar yau Laraba a Kano.
A cewar hukumar, marigayi Saminu Yusuf Abdullahi ya taka muhimmiyar rawa wajen sanar da al’umma ayyukan hukumar, musamman kan rigakafin tashin gobara, kai ɗaukin gaggawa da kuma kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
Rasuwarsa ta kasance babban rashi ga hukumar da al’umma baki ɗaya, duba da irin rawar da ya ke taka wa wajen isar da sahihan bayanai ga jama’a cikin gaggawa a lokutan aukuwar ibtila’i.
Solacebase








