Home Siyasa Kano: Majalisar dokoki ta gayyaci wakilin Nasarawa kan zarginsa da wulakanta Zomo

Kano: Majalisar dokoki ta gayyaci wakilin Nasarawa kan zarginsa da wulakanta Zomo

0
Majalisar Dokokin Jihar Kano ta gayyaci dan wakilin karamar hukumar Nassarawa a zauren Yusuf Bello Aliyu, domin ya bayyana kan wasu kalamai da yin bidiyon daga kunnuwan zomo da ake zargin ya yi, wadanda suka bazu a kafafen sada zumunta.
Shugaban majalisar, Alhaji Jibril Ismail Falgore, ne ya sanar da daukar matakin yayin zaman majalisar na Litinin din makon nan, sakamakon kudirin gaggawa da dan majalisa mai wakiltar Minjibir, Abdulhamid Abdul Minjibir, ya gabatar.
Abdulhamid Abdul Minjibir ya ce ya ga wani rubutu da Bello-Aliyu ya wallafa a kafafen sada zumunta, inda yake rike da kunnuwan zomo tare da furta kalaman da ya bayyana a matsayin wadanda ba su dace da matsayin dan majalisa ba.
Ya bukaci a mika lamarin ga kwamitin ladabtarwa na majalisa domin gayyatar dan majalisar ya yi bayani kan dalilin aikata hakan.
Shi ma Musa Ali-Kachako, mai wakiltar Takai, ya bukaci majalisar ta dauki matakin ladabtarwa bisa dokokinta, yana mai cewa ya kamata ‘yan majalisa su zama abin koyi ga al’umma.
A nasa bangaren, Usman Abubakar-Tasiu, mai wakiltar Kiru, ya nuna damuwa kan yadda ake amfani da kafafen sada zumunta wajen cin zarafi da zagin mutane, tare da bukatar samar da doka domin dai-daita amfani da su.
Daga karshe majalisar dokokin, ta umarci Yusuf Bello Aliyu, da ya gurfana a gaban kwamitinta na ladaftarwa a ranar Talata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here