Home Ilim Gwamnatin Kano ta aminta da sake duɗe Makarantar Prime College

Gwamnatin Kano ta aminta da sake duɗe Makarantar Prime College

0

Gwamnatin Jihar Kano ta amince da sake buɗe makarantar Prime College daga ranar Litinin, 23 ga watan Nuwamba, 2026, bayan shugabannin makarantar sun amince da alhakin kura-kuran gudanarwa da su ka jawo rufe makarantar na ɗan lokaci.

Sakataren zartarwa na Hukumar Kula da Makarantu Masu Zaman Kansu da na Sa-kai ta Jihar Kano KSPVIB, Baba Abubakar Umar, ne ya bayyana hakan yayin da ya ke zantawa da manema labarai a yau Juma’a.

Ya ce, amincewar sake buɗe makarantar na zuwa ne bisa sharaɗin cewa mahukuntanta za su kammala cika dukkan wasu ƙa’idoji da takardun shaidar gudanar da makaranta da hukumar ke buƙata.

Abubakar Umar ya bayyana cewa, hukumar ta rufe makarantar ne a ranar 18 ga watan Nuwamba, bisa dalilin rashin sabunta takardar shaidar izinin gudanar da ayyukanta kamar yadda dokokin hukumar su ka tanada.

Ya bayyana cewa matakin rufe makarantar ya kasance wani ɓangare na ikon da doka ta bai wa hukumar, ba wai da nufin hukunta makarantar ko kawo cikas ga karatun ɗalibanta ba.

Sakataren ya ce hukumar ta sake duba matakin ne bayan roƙon da wasu manyan mutane su ka gabatar, tare da neman afuwa da kuma amincewa da alhakin kura-kuran gudanarwa daga mahukuntan makarantar.

Ya ƙara da cewa an buƙaci makarantar ta kammala dukkan wasu buƙatun takardun shaidar gudanarwa da su ka rage tare da miƙa muhimman takardun da inganta tsarin gudanarwarta da kuma biyan dukkan kuɗaɗen da doka ta wajabta mata na shekarar karatu ta 2026/2027.

A cewarsa, sake buɗe Prime College ba ya na nufin hukumar ta sassauta ƙa’idojin da ta ke amfani da su wajen kula da makarantu ba ne, sai dai hakan na nuna jajircewarta wajen tabbatar da adalci da kuma kare muradun ɗalibai.

Ya jaddada cewa babu wata makaranta da ta fi ƙarfin doka, ba tare da la’akari da girmanta, alaƙarta da addini ko kuma irin tasirin da ta ke da shi a cikin al’umma ba, inda ya buƙaci dukkan makarantun masu zaman kansu da na sa-kai su kiyaye dokokin hukumar.

Baba Abubakar Umar, ya kuma bayyana cewa hukumar na da cikakken ikon doka na sanya ido kan harkokin makarantu, tare da rufe duk wata cibiya na wucin gadi ko na dindindin idan ta gaza bin dokoki da ƙa’idojin da aka gindaya.

Ya buƙaci masu makarantun masu zaman kansu a faɗin jihar su cika dukkan wajibai da dokokin hukumar suka ɗora musu, su kyautata alaƙarsu da iyayen ɗalibai, tare da tabbatar da cewa makarantu suna gudanar da ayyukansu bisa ƙa’idojin da aka amince da su.

Haka kuma, ya nuna damuwa kan yadda wasu makarantu ba su karɓi fom ɗin sabunta takardun shaidar gudanarwa ba, yayin da wasu da suka karɓa kuma suka gaza zuwa domin yin tambayoyin tantancewa da hukumar ta tanada.

Sakataren ya ce hukumar za ta fara gudanar da aikin tabbatar da bin dokoki ta hanyar kotun tafi-da-gidanka kafin ƙarshen watan Nuwamba, inda ya gargaɗi cewa duk makarantar da aka samu tana karya umarnin doka za ta fuskanci hukuncin da ya dace.

Ya tabbatar wa iyaye da ɗalibai cewa manufar hukumar ba ita ce rufe makarantu ba tare da wani dalili ba, sai dai tabbatar da cewa dukkan cibiyoyin ilimi suna bin ƙa’idojin da aka tsara domin inganta harkokin ilimi a jihar.

Haka kuma, Baba Abubakar Umar, ya jaddada cewa rufe Prime College na ɗan lokaci an yi shi ne domin tilasta wa mahukuntanta bin doka da ƙa’idojin gudanar da makarantu, ba wai domin tsoratar da su ba, yana mai kira ga masu makarantu da su mutunta ikon hukumar domin kauce wa fuskantar hukunci.

 

AhsantNews: Madogarar samun sahihan labarai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here