Dandazon magoya bayan darikar Kwankwasiyya, sun gudanar da zanga-zangar lumana tare da kai Ƙorafin hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya INEC kan rashin fitar da sunan dan takarar gwamnan Kano na jam’iyyar NDC na Jihar Kano, ta na neman a dawo da sunan ɗan takararta da aka cire daga jerin sunayen masu neman takarar a zaben badi.
Masu zanga-zangar, ƙarƙashin jagorancin mataimakin ɗan takarar gwamna, Mustapha Kwankwaso, wanda ya wakilci ɗan takarar Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, sun kai ƙorafin zuwa ofishin INEC na jihar, inda suka miƙa takardar neman a sake shigar da ɗan takararsu cikin jerin sunayen masu takara.
Mustapha Kwankwaso ya ce ƙungiyar ta cika dukkan ƙa’idoji da dokokin da hukumar zaɓen ta gindaya game da tsayar da ‘yan takara, ya na mai bayyana cire sunan ɗan takararsu a matsayin abin da bai dace ba.

Da ya ke jawabi ga masu zanga-zangar, Kwamishinan Zaɓe na INEC a Kano, Abdu Zango, ya ce, hukumar ta fahimci dalilin da ya jawo cire sunayen, ya na mai cewa har yanzu akwai damar ɗaukaka ƙara zuwa ranar 24 ga watan Oktoba.
Zango ya ce, hukumar ta karɓi dukkan ƙorafe-ƙorafen da aka gabatar mata, tare da tabbatar wa tawagar cewa za a duba takardar ƙorafin yadda ya kamata, sannan a tura ta zuwa babban ofishin hukumar na ƙasa domin nazari da ɗaukar matakin da ya dace.
Ya kuma jaddada cewa ofishin INEC na Kano ba ya goyon bayan wani ɓangare, ya na mai yaba wa masu zanga-zangar bisa yadda suka gabatar da ƙorafinsu cikin lumana da tsari, ba tare da amfani da tashin hankali ba.
A wani ɓangaren kuma, mai magana da yawun ƙungiyar Kwankwasiyya, Dr. Habib Mohammed, ya ce, ƙorafin bai tsaya kawai kan cire sunan ɗan takararsu ba, domin ya ƙunshi zargin ƙirƙirar takardun bogi da kuma haɗin baki da wani ma’aikacin INEC da ake zargi.
Dr. Mohammed ya yi zargin cewa an miƙa wasu wasiƙu zuwa babban ofishin INEC ba tare da izinin waɗanda doka ta amince su yi hakan ba, kuma wasu daga cikin wasiƙun na ɗauke da sa hannun da ake zargin na bogi ne. Ya ce hakan ne ya haifar da sauya sunayen wasu daga cikin ‘yan takararsu a Kano.
Ya bayyana cewa ƙungiyar ta buƙaci INEC ta gudanar da bincike kan ma’aikacin da ake zargi kafin ɗaukar wasu matakai, yana mai cewa sun gamsu da tabbacin da Kwamishinan Zaɓen ya ba su na cewa zai miƙa ƙorafin zuwa babban ofishin hukumar.
A nasa ɓangaren, Abdu Zango ya ce INEC za ta ba ƙorafin kulawar da ta dace, tare da miƙa shi ga hedikwatar hukumar domin duba shi da kuma yin abin da ya dace bisa ƙa’idojin hukumar.
Baya ga batun ƙorafin, Kwamishinan Zaɓen ya kuma yi magana kan ci gaba da karɓar katin zaɓe na dindindin (PVC), wanda aka fara ranar 9 ga watan Oktoba, inda ya bayyana gamsuwarsa da yadda jama’a ke fitowa domin karɓar katunansu.
Ya kuma ce hukumar na shirin faɗaɗa wuraren karɓar katin zaɓen zuwa yankunan rajista domin sauƙaƙa wa al’umma samun katunansu.








