Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta tabbatar da rasuwar Sheikh Yahaya Masussuka, wanda ake zargin wasu ’yan bindiga da ke kan babur sun harbe shi a kofar gidansa, da ke garin Dutsinma a daren Litinin, wanda hakan ya yi sanadiyar rasuwarsa.
Maharan, sun hallaka marigayin ne tare da wani abokinsa da ya kai masa ziyara.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 9 na dare a ƙofar gidan malamin, lokacin da maharan suka buɗe masa wuta tare da aminin nasa.
Bayan harin, an garzaya da su zuwa Asibitin Dutsin-Ma domin samun agajin gaggawa, amma daga bisani aka tabbatar da rasuwarsu.
Ya zuwa yanzu, ba a samu cikakken bayani kan dalilin kisan ko waɗanda suka aikata shi ba.
Lamarin ya jefa al’ummar Dutsin-Ma cikin alhini, musamman mabiyan Sheikh Yahaya Masussuka da sauran waɗanda suka san shi a cika da wajen Najeriya.








