Home Ilim Gwamna Abba Kabir ya amince da ƙarin albashi ga ma’aikatan Jami’o’in Northwest...

Gwamna Abba Kabir ya amince da ƙarin albashi ga ma’aikatan Jami’o’in Northwest da Wudil 

0

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da sabon tsarin ƙarin albashi ga malaman jami’a da ma’aikatan da ba malamai ba na Jami’ar Aliko Dangote ta Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, da Jami’ar Northwest da ke Kano.

Sabon tsarin albashin ya samo asali ne daga tsarin albashin da gwamnatin tarayya ta amince da shi kuma take amfani da shi a jami’o’in tarayya.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da daraktan janar na yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na Gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ranar Litinin.

Sanarwar ta ce, amincewar ta biyo bayan rahoto da shawarwarin wani kwamiti da Majalisar Zartarwar Jihar Kano ta kafa domin duba buƙatar jami’o’in biyu na amfani da sabon tsarin albashin.

A cewar sanarwar, sabon tsarin albashin zai fara aiki daga watan Janairun 2026, yayin da za a fara biyan sabon albashin daga watan Satumban 2026.

Jimillar kuɗin da sabon tsarin zai ci a kowane wata ga jami’o’in biyu ya kai Naira miliyan 391.85, wanda ya kai kusan Naira biliyan 4.70 a shekara.

A Jami’ar Aliko Dangote da ke garin Wudil, sabon tsarin zai ci Naira miliyan 228.20 a wata, inda Naira miliyan 141.08 za ta tafi ga malaman jami’a bisa yarjejeniyar ASUU, yayin da Naira miliyan 87.11 za ta tafi ga ma’aikatan da ba malamai ba bisa tsarin SSANU.

A Jami’ar Northwest kuwa, kuɗin zai kai Naira miliyan 163.65 a wata, wanda ya haɗa da Naira miliyan 112.24 ga malaman jami’a da Naira miliyan 51.41 ga ma’aikatan da ba malamai ba.

Gwamnatin jihar ta kuma amince da ware Naira biliyan 1.57 a cikin kwaryakwaryar kasafin kuɗin shekarar 2026 domin biyan albashin daga Satumba zuwa Disamba 2026.

Haka kuma, za a tanadi Naira biliyan 3.13 a cikin kasafin kuɗin shekarar 2027 domin biyan bashin albashin da ya taso daga Janairu zuwa Agustan 2026.

Kwamitin ya ce matakin zai taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya tsakanin gwamnati da ma’aikata, da kuma inganta jin daɗin ma’aikatan jami’o’in biyu.

Haka kuma, Gwamnan, ya amince da duba yiwuwar kafa kwamitocin binciken aiki watau Visitation Panels ga jami’o’in biyu da sauran manyan makarantun jihar, kamar yadda dokokin da suka kafa makarantun suka tanada.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here