Home Labarai Muna kira ga Sarkin Takutahar ƙasar Hausa ya yi duk abinda ya...

Muna kira ga Sarkin Takutahar ƙasar Hausa ya yi duk abinda ya kamata don kawo wa Najeriya ci gaba– Sarkin Daura

0

Mai Martaba Sarkin Daura Alhaji Dakta Umar Farouk, ya buƙaci Sarkin Takutahar Ƙasar Hausa Sheikh Abdulkadir Jiyali ya yi dukkan abinda ya kamata domin kawo wa Najeriya ci gaba.

Sarkin na Daura ya bukaci hakan ne lokacin da yake nada shi a Matsayin Sarkin Takutahar Kasar Hausa na farko a tarihin Masautun Kasar Hausa a Najeriya.

Alhaji Dakta Umar Farouk yace Sheikh Jiyali ya cancanci bashi wannan sarauta ne bisa la’akari da yadda yake hidimtawa Al’uma da cusawa Matasa Soyayyar Annabi Muhammadu SAW.

Adon haka ne Sarkin na Daura ya bukaci Sarkin Takutahar ya cigaba da Mai da hankali ga dukkan abunda zai kawo Zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakanin Al’uma.

Alhaji Dakta Umar Farouk yayi kira da ya cigaba da yin biyayya bisa ga wannan Shugabanci da aka dora masa tareda hada kan Matasa.

A nasa bangren Sarkin Takutahar Kasar Hausa Sheikh Jiyali Abdulkadir ya godewa Mai Martaba Sarkin Daura Alhaji Dakta Umar Farouk bisa wannan Sarauta da aka naɗa shi tare da tabbatar da cewa zai ɗora tare da jajircewa akan yadda aka saba tare da ƙara Tsaftace harkar Takutaha.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here