Home Labarai Karin yan Najeriya 40 sun sauka a Lagos bayan kwaso su daga...

Karin yan Najeriya 40 sun sauka a Lagos bayan kwaso su daga Afirka ta Kudu

0

 

Wasu ’yan Najeriya 40 da aka kwaso daga kasar Afirka ta Kudu sun isa filin jirgin sama na birnin Lagos.

Hakan ya tabbatar da cewa, jimillar mutanen da aka dawo da su a rukuni na shida ya zama mutane 1,174.

Hukumar ’Yan Najeriya Mazauna Ƙasashen Waje (NiDCOM) ta ce mutanen sun isa ne cikin wani jirgin haya.

Waɗanda aka kwaso sun nuna godiyarsu ga Shugaba Bola Tinubu bisa amincewa da dawo da su cikin gaggawa, tare da yabawa duk masu ruwa da tsaki da suka taimaka wajen gudanar da aikin.

NiDCOM ta ce gwamnatin Jihar Imo ta bai wa mutanen jihar da suka dawo tallafin naira miliyan ɗaya kowannensu, yayin da kamfanin MTN ya ba su layukan waya da data kyauta tare da alƙawarin tura naira 100,000 ga kowane mutum.

Haka kuma, gwamnatocin jihohin Edo da Delta da wasu ƙungiyoyi sun sanar da shirye-shiryen tallafa wa waɗanda aka dawo da su din.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here