Home Labarai Zaɓen 2027: KOMC da Gidauniyar AMG sun horas da ƴan jarida kan...

Zaɓen 2027: KOMC da Gidauniyar AMG sun horas da ƴan jarida kan ɗakko rahoto yayin zaɓe

0
Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Najeriya NUJ sashen ƙungiyar masu yaɗa labarai ta ƙafar Internet (KOMC) tare da haɗin gwiwar Aminu Magashi Garba (AMG) Foundation, sun shirya taron horaswa na kwana guda domin ƙarfafa ƙwarewar ‘yan jarida kan yadda za su gudanar da rahotannin zaɓe cikin gaskiya, adalci da bin ƙa’idojin aikin jarida, tare da kare lafiyarsu gabanin babban zaɓen Najeriya na shekarar 2027.

Taron, wanda aka gudanar a ranar Laraba a Sakatariyar NUJ da ke Farm Centre a Kano, ya haɗa ‘yan jaridun kafafen yaɗa labarai na intanet daban-daban.

An mayar da hankali ne kan ɗabi’un aikin jarida, tantance sahihancin bayanai (fact-checking), rahotannin zaɓe da kuma hanyoyin kare kai yayin gudanar da aiki a lokutan zaɓe.

Da yake gabatar da nasa jawabi, gogaggen ɗan jarida kuma Mamallakin ƙafar yaɗa labarai ta SolaceBase, Kwamared Abdullateef Abubakar Jos, ya buƙaci ‘yan jarida su gudanar da aikinsu cikin ƙwarewa, gaskiya, riƙon amana da cikakken kishin ƙasa.

Ya bayyana cewa masu ɗaukar rahotannin zaɓe kan fuskanci barazana daga ‘yan daba da wasu jami’an tsaro, saboda haka ya kamata su yi amfani da dabarun kariya da ilimin da suka samu a irin wannan horaswa domin kare kansu yayin sauke nauyin da kundin tsarin mulki ya ɗora musu.

Da ya ke gabatar da muƙalarsa mai taken “Ɗabi’u, Tantance Sahihancin Bayanai da Rahoton Zaɓe,” tsohon Shugaban NUJ na Jihar Kano, Kwamared Abbas Ibrahim, ya jaddada muhimmancin daidaito, adalci da rashin son kai wajen bayar da rahotannin zaɓe.

Ya kuma yi gargaɗi kan yaɗa labaran ƙarya da bayanan da ba a tantance ba, yana mai kira ga ‘yan jarida su tsaya tsayin daka wajen kare martabar aikin jarida.

Shi ma ƙwararren ɗan jarida Isyaku Ahmad da ya gabatar da muƙala ya yi bayani kan muhimmancin bin ƙa’idojin aikin jarida kafin, lokacin da kuma bayan zaɓe.

Ya kuma yi wa mahalarta bitar wasu dabaru da za su taimaka musu wajen fuskantar ƙalubalen da kan taso yayin ɗaukar rahotannin zaɓe da rikice-rikice.

A jawabinsa na maraba, Shugaban NUJ Kano Online Media Chapel, Kwamared Abubakar Abdulkadir Dangambo, ya bayyana cewa horaswar za ta ƙara wa mahalarta ƙwarewa wajen samar da rahotanni masu sahihanci, aminci da kauce wa tayar da rikici yayin babban zaɓen shekarar 2027.

Taron ya kasance wani ɓangare na ƙoƙarin da Kano Online Media Chapel da Aminu Magashi Garba Foundation ke yi na inganta aikin jarida, yaƙi da yaɗa bayanan ƙarya, da kuma ƙarfafa tsaro da ƙwarewar ‘yan jarida domin su taka rawar da ta dace wajen ƙarfafa dimokuraɗiyya a Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here