Gwamnatin jihar Kano ta ƙarkashin ma’aikatar lafiya, ta umarci hukumar kula da asibitoci masu zaman kansu PHIMA, da ta kulle dukkan wani asibitin kuɗi da ke yin aiki ba tare da ya yi Rijista ba.
Kwamishinan lafiya Dakta Abubakar Labaran Yusuf, ne ya bada wannan umarni yayin da ya ke buɗe taron bita da bada horo ga shugabanni da mamallaka asibitoci masu zaman kansu da ke nan Kano wanda hukumar kula da asibitoci masu zaman kansu PHIMA ta shirya, ake gudanar da shi yanzu haka a yau Alhamis.
Ya ce, ɗaukar wannan mataki ya zama dole sakamakon yadda ake samun matsaloli wajen yadda asibitocin ba sa gabatar wa gwamnatin bayanan ayyukansu kama daga alƙaluma da bayanan mutanen da suka duba da sauransu.
Kwamishinan, ya ƙara da cewa, “A yanzu haka mutane da dama sun zaɓi riƙa tafiya asibitoci masu zaman kansu maimakon na gwamnati domin neman lafiya, sai dai da da dama daga cikin irin waɗannan asibitoci ba su da Rijista.
Don haka daga yanzunan, ina mai sanar da bayar da umarnin kulle duk wani asibiti da ke gudanar da aiki ba tare da cikakkiyar rijistar gwamnati ba.”








