An gudanar da jana’izar wasu yara Almajirai guda hudu wadanda suka rasu sakamakon cin wani abinci da ake zargin cewa gurbatacce ne.
Shugaban ƙungiyar Tsangaya Media Network ta Najeriya Alaramma Malam Sani Musa Nuhu, ne ya tabbatar hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar.
Ya ce, Almajiran huɗu sun kasance yan Tsangayar Malam Iliyasu da ke Kadage Sharifai a Ƙaramar Hukumar Ungogo.
Haka kuma, ta cikin sanarwar, ya ƙara da cewa, an gudanar da jana’izar almajiran bayan samun umarni daga Dagaci da baturen ƴan snadan yankin.
Sanarwar ta kuma ce, almajiran sun rasu ne a Asibitin koyarwa na Aminu Kano a daren jiya Lahadi.








