Home Labarai PCACC ta cafke mutumin da ake zargi da sayar da kadarar gwamnatin...

PCACC ta cafke mutumin da ake zargi da sayar da kadarar gwamnatin Kano

0

Hukumar Korafe-korafe da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Kano, PCACC, ta kama wani mutum mai suna Tasiu Adamu Maje, bisa zarginsa da sayarwa da kuma bayar da hayar wani wurin ajiye dawaki mallakar gwamnatin jihar Kano, da ke Filin Sukuwa.

A cewar hukumar, kama mutumin ya biyo bayan korafe-korafen da Muhammad Amir Yunusa da Usman Bala Yakasai, wanda aka fi sani da Sharif, suka shigar, su na zargin cewa wanda ake zargin ya miƙa tare da bayar da kadarar ga wasu mutane masu zaman kansu ba tare da izinin hukuma ba.

Shugabar riko ta hhugabar PCACC, Hafsat Ada’u Kutama, ta ce, binciken hukumar ya gano cewa Hukumar Wasanni ta Kano, wadda ke da alhakin kula da rabon wuraren ajiye dawaki a jihar, ba ta san da cinikin ba kuma ba ta bayar da izinin gudanar da shi ba.

Hukumar ta ce babu wani mutum da aka ba wannan wurin a hukumance ta hanyar sayarwa ko haya, yayin da takardar da wanda ake zargin ya yi amfani da ita wajen cinikin ba ta cikin takardun da Hukumar Wasanni ta Kano ta amince da su.

PCACC ta kuma ce ana zargin Tasiu Adamu Maje ya sayar da wurin ga Muhammad Amir Yunusa kan Naira miliyan 4 da rabi, yayin da a lokaci guda yake karɓar kuɗin haya daga Usman Bala Yakasai, inda aka ce an biya Naira dubu 150 daga cikin Naira dubu 180 da aka nema.

Hukumar ta bayyana mu’amalolin a matsayin marasa izini kuma marasa inganci, tana mai cewa kadarar har yanzu mallakin gwamnatin Kano ce kuma tana ƙarƙashin kulawar Hukumar Wasanni ta jihar.

PCACC ta ce tana ɗaukar matakan dawo da kadarar, yayin da ake sa ran gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu domin a bi matakan shari’a.

Hukumar ta gargadi jama’a da su guji shiga harkar saye ko haya ta kadarorin gwamnati ba tare da tabbatar da mallaka da sahihancin takardun kadarar daga hukumomin da abin ya shafa ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here