Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya nada Barrister Hafsat Ada’u Kutama a matsayin shugabar Hukumar karbar korafi da yaki da cin hanci da rashawa PCACC.
Mai bai wa gwamnan shawara kan kafafen sada zumunta, Ibrahim Adam, ne ya bayyana hakan a shafinsa na sada zumunta a yau Laraba.
Ya ce, kafin nadin, Barrister Hafsat Kutama ita ce, Sakatariyar hukumar.
Nadin dai ya biyo bayan rahoton murabus din tsohon shugaban hukumar, Saidu Yahaya, wanda aka ce ya ajiye mukaminsa yau Talata.








