Gwamnan Jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya kafa kwamiti mai ba da shawara domin binciken cece-ku-ce da suka biyo bayan wasu kalamai da ake zargin wasu malaman addinin Musulunci sun yi a jihar, wadanda gwamnati ta ce sun taimaka wajen kawo rashin jituwa.
A cewar sanarwar da Daraktan Yaɗa Labarai na Gidan Gwamnatin Sokoto, Abubakar Bawa, ya fitar ranar 15 ga Satumba, cece-kucen ya fi mayar da hankali kan kalaman da ake dangantawa da malamin addinin Musulunci, Malam Musa Lukuwa, wadanda suka jawo sabani tsakanin wasu al’ummar Musulmi a jihar.
Kwamitin zai kasance karkashin jagorancin Malam Yahaya na Malam Boyi, tare da wakilan kungiyoyin addinin Musulunci da suka hada da Izala daga Kaduna da Jos, Tijjaniyya, Ƙadiriyya, Jama’atu Nasril Islam da Majalisar Sarkin Musulmi, da kuma Kwamishinan Harkokin Addini na jihar.
Gwamnatin ta umarci kwamitin da ya duba matsayar Shari’a kan batutuwan da Malam Musa Lukuwa ya yi magana a kansu, sannan ya bai wa gwamnati shawarwari.
An ba kwamitin wa’adin kwanaki 14 domin gabatar da rahotonsa.








