Home Labarai Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Kano ya yi...

Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Kano ya yi murabus

0

Wasu rahotonni sun tabbatar da cewa shugaban hukumar karbar korafi da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano watau PCACC, Kwamared Saidu Yahaya, ya sauka daga mukaminsa.

Kafar yada labarai ta Freedom Radio ta ruwaito cewa, Kwamared Saidu Yahaya, ya tabbatar ma ta da yin murabus dinsa a yau Laraba.

Sai dai wasu Majiyoyi sun ce, murabus din nasa ya biyo bayan matsin lamba da ya ke fuskanta daga gwamnatin jihar Kano, kan zargin nuna damuwa game da biyayyarsa ta siyasa da kuma alakarsa da tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Tun a watan Agustan shekarar 2025 ne Gwamana Abba Kabir Yusuf ya nada Kwamared Sa’idu Yahaya a matsayin shugaban hukumar ta PCACC, bayan karewar wa’adin tsohon shugaban hukumar, Muhyi Magaji Rimin Gado.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here