Tsohon Darakta Janar na Hukumar jin daɗin Alhazai ta jihar Kano, Alhaji Sani Lawan Ƙofar Mata, ya rasu.
Rahotonni sun bayyana cewa, Alhaji Sani Lawan Ƙofar Mata ya rasu ne da yammacin yau Lahadi a Kano, sakamakon rashin lafiyar da ya yi fama da ita.
Marigayin ya kasance makusanci ga tsohon Gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau, a jam’iyyar ANPP, inda ya taka muhimmiyar rawa a lokacin zaɓen gwamnan Kano na shekarar 2007.
A shekarar 2011 ne Sani Lawan Ƙofar Mata ya fice daga jam’iyyar ANPP tare da wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar kafin daga bisani ya koma jam’iyyar ACN.
Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa, za a gudanar da jana’izarsa da ƙarfe 9:00 na safiyar gobe Litinin, a gidansa da ke Kano.








