Home Labarai Najeriya da Saudiyya sun sanya hannu kan yarjejeniyar haɗin gwiwa a fannin...

Najeriya da Saudiyya sun sanya hannu kan yarjejeniyar haɗin gwiwa a fannin tsaro

0

Wata sanarwa da Mataimaki na Musamman kan yaɗa labarai ga Karamin Ministan tsaro, Ahmed Dan Wudil, ya fitar a ranar Talata ta bayyana cewa yarjejeniyar za ta mayar da hankali kan horar da sojoji, musayar bayanan sirri, inganta tsaro da kuma gudanar da ayyukan hadin gwiwa.

An sanya hannu a yarjejeniyar ne a birnin Riyadh na Saudiyya, tsakanin Karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, da takwaransa na Saudiyya, Dr. Khaleed Al-Biyari.

A cewar sanarwar, ana sa ran wannan yarjejeniya za ta kafa tubalin ci gaban tsaro mai dorewa da zai kara karfafa dangantakar diflomasiyya da tsaro tsakanin kasashen biyu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here