Wata sanarwa da Mataimaki na Musamman kan yaɗa labarai ga Karamin Ministan tsaro, Ahmed Dan Wudil, ya fitar a ranar Talata ta bayyana cewa yarjejeniyar za ta mayar da hankali kan horar da sojoji, musayar bayanan sirri, inganta tsaro da kuma gudanar da ayyukan hadin gwiwa.
An sanya hannu a yarjejeniyar ne a birnin Riyadh na Saudiyya, tsakanin Karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, da takwaransa na Saudiyya, Dr. Khaleed Al-Biyari.
A cewar sanarwar, ana sa ran wannan yarjejeniya za ta kafa tubalin ci gaban tsaro mai dorewa da zai kara karfafa dangantakar diflomasiyya da tsaro tsakanin kasashen biyu.








