Home Labarai An shiga halin juyayi a Kano sakamakon kashe jami’in NSCDC da ƴan...

An shiga halin juyayi a Kano sakamakon kashe jami’in NSCDC da ƴan daba suka yi

0

An shiga halin juyayi da alhini a jihar Kano ranar Juma’a bayan kashe wani jami’in sa-kai na Hukumar Tsaro Civil Defence NSCDC, Abdurrauf Sheriff, wanda ake zargin wasu ‘yan daba sun daɓa masa wuƙa yayin da ya ke gudanar da aiki a hukumance.

Lamarin ya faru ne a titin Gyadi-Gyadi Court Road, inda rahotonni suka ce marigayin ya na cikin aikin sa lokacin da ‘yan daban suka kai masa hari yayin bikin sabuwar shekara da Gwamnan Kano ke gudanarwa.

A cikin wata sanarwa da ta tabbatar da faruwar lamarin, Rundunar NSCDC ta Kano ta bayyana kisan a matsayin danyen aiki da rashin imani da aka aikata kan jami’in da ke bakin aiki cikin doka.

Sanarwar, wadda jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar, Ibrahim Abdullahi, ya fitar, ta bayyana cewa an kama mutane huɗu da ake zargi da hannu a cikin lamarin.

“Rundunar na sanar da jama’a cewa an kama mutane huɗu da muggan makamai ciki har da gatari, Danbida da miyagun ƙwayoyi. Su na hannun hukuma kuma suna taimakawa wajen bincike domin ganin an tabbatar da adalci,” in ji Abdullahi.

A cikin martaninsa kan wannan mummunan al’amari, Kwamandan NSCDC na Kano, Commandant Mohammed Hassan Agalama, ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan mamacin tare da tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da tsayawa wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Ya kuma jaddada aniyar NSCDC na yin aiki kafada da kafada da sauran hukumomin tsaro domin yaki da aikata laifuka a jihar.

A cewar sanarwar, binciken farko ya nuna cewa lamarin na da nasaba da kisan kai, kuma za a mika masu lefin hannun ‘yan sanda domin zurfafa bincike da gurfanar da wadanda ake zargi a kotu.

Rundunar ta kuma bukaci jama’a da su kwantar da hankalinsu tare da ci gaba da ba da goyon baya ta hanyar samar da sahihan bayanai a kan lokaci domin sauƙaƙa aikin yaƙi da laifuka a fadin jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here