Home Labarai Babban layin wutar lantarkin Najeriya ya sake lalacewa

Babban layin wutar lantarkin Najeriya ya sake lalacewa

0

Babban layin wutar lantarki na Najeriya, ya sake lalacewa a yammacin yau Litinin, lamarin da ya sa aka samu matuƙar ƙarancin wutar lantarki a mafi yawan sassan ƙasa kamar yadda alkaluman rarraba wuta da kamfanonin rarraba wutar lantarki suka bayyana da misalin ƙarfe 3:12 na rana.

Haka kuma, bayanai daga kamfanonin rarraba wutar lantarki sun nuna cewa kamfanoni biyu ne kaɗai suka samu wuta bayan lalacewar babban layin wutar kamfanin rarraba wutar lantarki na Ibadan ya samu megawatt 30, yayin da kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja ya samu megawatt 20.

Sauran kamfanonin rarraba wutar lantarki na Benin da Eko da Enugu da Ikeja da Jos da Kaduna sa Kano da Port Harcourt da kuma Yola duk ba su samu ko da megawatt ɗaya ba.

Jimillar wutar lantarki da aka rarraba a Najeriya baki ɗaya a lokacin ta tsaya ne a megawatt 50 kawai, wanda ya yi ƙasa da matakin aiki na yau da kullum kuma bai isa ya wadatar da gidaje, kasuwanci da guraren ayyuka.

A baya-bayan nan, babban layin wutar lantarki na ƙasa ya sha fuskantar rushewa sau da dama, lamarin da ke haddasa katsewar wuta a faɗin ƙasa tare da jinkirin dawo da wutar.

A halin yanzu dai, kamfanin wutar lantarki na ƙasa NNG ya bayyana cewa, ana ci gaba da aikin gyarawa tare da dawo da wutar lantarkin.

Solacebase

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here