Home Labarai Yadda Anthony Joshua ya tsallake Rijiya da baya a hatsarin mota

Yadda Anthony Joshua ya tsallake Rijiya da baya a hatsarin mota

0

Wani hatsarin mota da ya afku a Ogun ya rutsa da shahararren ɗan damben duniya, Anthony Joshua yau Litinin a yankin Makun na jihar, a kan babbar hanyar Lagos zuwa Ibadan.

Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa, mutane biyu sun rasa rayukansu sakamakon hatsarin, yayin da Anthony Joshua, kuma ya samu raunuka.

Ta kuma ruwaito cewa, motar da ke ɗauke da Antnony Joshua, ƙirar Lexus Jeep mai lambar rajista KRD 850 HN, ta bugi wata babbar mota ne wadda ke tsaye a gefen hanya.

Hatsarin ya faru ne kusa da gidan mai na Danco da ke kan babbar hanyar Lagos zuwa Ibadan a jihar Ogun.

Jami’in wayar da kan jama’a na hukumar kiyaye haɗurra ta tarayya a jihar Ogun, Afolabi Odunsi, ya tabbatar da faruwar hatsarin, inda ya bayyana cewa Anthony Joshua ya na raye duk da raunukan da ya samu, yayin da mutane biyu suka mutu a hatsarin.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here