Home Labarai Binciken EFCC a kaina ba shi da alaƙa da zargin ta’addanci- Abubakar...

Binciken EFCC a kaina ba shi da alaƙa da zargin ta’addanci- Abubakar Malami

0

Tsohon Babban lauyan gwamnatin tarayya, Abubakar Malami SAN, ya musanta rahotannin da ke cewa yana fuskantar bincike kan ta’addanci, safarar kuɗi da kuma mallakar asusun banki da dama.

Malami ya bayyana cewa tambayoyin da Hukumar EFCC ta yi masa sun shafi zargin sake dawowar kuɗaden Abacha ne kaɗai, ba wani abu makamancin haka ba.

A wata sanarwa da ofishinsa ya fitar a Larabar makon nan, Abubakar Malami ya ce, EFCC ta gayyace shi ne domin ya fayyace batun zargin cewa an maimaita dawo da dala miliyan 310 na kuɗaɗen Abacha a lokacin gwamnatin marigayi Shugaba Muhammadu Buhari.

Ya ce bayan bayanin da ya gabatar, hukumar ta fahimci cewa ba a ma kammala dawo da kuɗin a lokacin da ake zargin an yi maimaitawar ba.

Malami ya kuma nuna cewa, takardun lauya Enrico Monfrini tun a shekarar 2016 sun tabbatar da cewa ba a aiwatar da maimaitawar da ake zargi ba.

Ya ƙara da cewa, gwamnatin Buhari ta ƙi amincewa da tsarin karɓar kuɗaɗen da Monfrini ya nemi ya ci gaba da jagoranta, inda ta zaɓi lauyoyi ’yan Najeriya waɗanda suka taimaka wajen ƙwato makudan kuɗaɗe na ƙasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here