Home Labarai Tinubu ya gargaɗi hukumomin tsarokan su gaggauta cire ƴan Sanda daga rakiya...

Tinubu ya gargaɗi hukumomin tsarokan su gaggauta cire ƴan Sanda daga rakiya VIPs

0

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sake jan hankalin hukumomin tsaro da su gaggauta aiwatar da umarninsa na cire ’yan sanda daga rakiya da manyan mutane watau VIPs.

Shugaban, ya bayyana hakan ne yayin zaman Majalisar Zartarwa ta Tarayya, inda ya nuna rashin jin daɗinsa kan jinkirin aiwatar da tsarin da ya tsara domin ƙarfafa tsaron tituna da yankuna.

Tinubu ya umarci Ministan cikin cida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, da babban Sufeton Ƴan sanda Kayode Egbetokun da shugaban Hukumar tsaro ta NSCDC su tsara yadda za a maye gurbin jami’an da za a cire ba tare da barin jama’a cikin haɗari ba.

Ya ce wajibi ne a tura jami’an tsaro zuwa wuraren da ake buƙata, tare da ba da makamai ga Forest Guards domin hana sace-sacen mutane da barna a dazuzzuka.

Ya kuma jaddada cewa duk VIPs da ke buƙatar kariya su koma amfani da Civil Defence, kamar yadda umarninsa na 23 ga Nuwamba ya tanada.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here