Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya shigar da ƙorafi ga Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da sauran Laifuka Masu Alaƙa ta Ƙasa ICPC a kan daraktan gudanarwa na Hukumar Kula da harkokin Man Fetur da ƙayyade farashi ta Ƙasa NMDPRA, Farouk Ahmed, bisa zargin cin hanci da almundahanar kuɗi.
A cikin ƙorafin da ya gabatar, Dangote ya nemi a kama Farouk Ahmed, a bincike shi tare da gurfanar da shi, bisa zargin rayuwa fiye da halin samun kuɗin halal a matsayinsa na ma’aikacin gwamnati.
Dangote ya bayyana cewa Farouk Ahmed ya kashe kuɗi sama da dalar Amurka Miliyan Bakwai wajen biyan kuɗin karatun ’ya’yansa huɗu a makarantu daban-daban a ƙasar Switzerland tsawon shekaru shida gaba ɗaya, ba tare da hujjar tushen halal na kuɗin ba.
Ƙorafin ya ƙunshi sunayen ’ya’yan da makarantar kowane ɗaya ke karatu da kuma adadin kuɗin da aka biya, domin bai wa hukumar yaƙi da cin hanci damar tantance gaskiyar zarge-zargen da kuma tabbatar da su.
Dangote ya kuma bayyana cewa Farouk Ahmed yana amfani da ikon hukumar NMDPRA wajen karkatar da kuɗaɗen jama’a don amfanin kansa da biyan buƙatun sirri, lamarin da ya janyo ƙorafi da zanga-zanga daga ƙungiyoyi daban-daban a baya-bayan nan.
Ya ƙara da cewa duk tsawon rayuwar Farouk Ahmed a matsayin baligi, aikinsa yana cikin ɓangaren gwamnati ne, kuma jimillar abin da ya samu a matsayin albashi ba zai kai adadin kuɗin da aka kashe wajen karatun ’ya’yansa a ƙasashen waje ba.
Dangote ya jaddada cewa ICPC na da ikon doka na bincike da gurfanar da duk wanda aka samu da laifin cin hanci, almundahanar kuɗi da cin zarafin mukami, tare da kira ga hukumar da ta ɗauki mataki cikin gaggawa domin kare martabar mulkin Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da kuma tabbatar da adalci ga ’yan Nijeriya.
Yayin da Majalisar Wakilai ta shiga tsakani ta gayyaci bangarorin biyu domin warware rikicin da ya kunno kai.
Sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoto hukumar NMDPRA da kuma shugaban nata Farouk Ahmed ba su fitar da wata sanarwa ba kan lamarin.
Solacebase








