Home Labarai DSS ta bai wa Fulani diyyar Miliyan 3 bayan ta tsare su...

DSS ta bai wa Fulani diyyar Miliyan 3 bayan ta tsare su na fiye da shekara 1 ba bisa ka’ida ba

0

Humumar tsaro ta DSS ta saki wasu mutane uku Fulani da ta kama yayin da suke sauka acikin jirgi bayan sun dawo daga aikin Hajji a watan yunin 2024

DSS ta bayyana hakan ne a wani taron manema labarai a hedikwatar ta dake Abuja inda ta ce ta kama mutanen ne bisa zargin su da hannun su a ayyyukan garkuwa da mutane a arewacin kasar nan

Wadanda hukumar ta kama sun hadar da Rabi’u Alhaji Bello da umar Ibrahim da Bammo Jajo Sarki dukan su yan jihar kwara 

Hukumar ta DSS ta ce ta kammala bincike a kan su kuma bata same su da laifin komai ba hakan ce ta sa ta baiwa kowannen su kyautar naira miliyan daya 

Kungiyoyin Fulani sun sha kokawa kan kama mutanensu game da zargin garkuwa da mutane da kuma ta’adanci ba tare da wata hujja ba inda sukace hakan abin takaici ne 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here