Home Nishaɗi Yan sandan Hong Kong sun cafke fasinjan da ya yi yunkurin bude...

Yan sandan Hong Kong sun cafke fasinjan da ya yi yunkurin bude jirgin sama yayin da ya ke tafiya

0

Jami’an yan sandan Hong Kong sun cafke wani fasinja bisa laifin yunkurin bude kofar jirgin sama, lokacin da yake tsaka da tafiya a sararin samaniya, bayan taso wa daga birnin Boston na kasar Amurka, a kan hanyar zuwa Hong Kong.

Rahotonni sun bayyana cewa, Kamfanin jirgin mai suna Cathay Pacific, ya sanar da cewa a yayin faruwar wannan balahira, babu wani fasinja ko ma’aikacinsa da ya samu rauni, kuma jirgin ya sauka lafiya.

Tuni dai jami’an yan sandan suka fara gudanar da bincike bayan cafke matashin da ake zargi da wannan yunkurin aikata wannan katobara.

Matashin da ake hutuma din, wanda ya kasance mai shekaru 20 dan asalin kasar China ne.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here