Home Labarai Jam’iyyar PDP ta tabbatar da mutuwar Mataimakin Gwamnan Bayelsa

Jam’iyyar PDP ta tabbatar da mutuwar Mataimakin Gwamnan Bayelsa

0

Jam’iyyar PDP ta tabbatar da mutuwar Mataimakin Gwamnan Jihar Bayelsa Lawrence Oboraw-Harievwo Ewhrudjakpo a yau Alhamis bayan matsalar lafiya da ta taso masa.

Tun da safiyar ranar damuwa ta karu kan lafiyarsa yayin da bayanai suka nuna cewa ya fadi ba tare da ya farfaɗo ba, lamarin ya janyo tashin hankali a cikin jihar da cikin jam’iyyar.

A cikin sanarwar da jam’iyyar PDP wadda mai jagorancinta Tanimu Turaki ta fitar, ta bayyana mutuwar tasa a matsayin babban rashi wanda ya girgiza dukkan ‘ya’yan jam’iyyar musamman na Bayelsa.

Gwamnatin Jihar Bayelsa bata fitar da sanarwa ta hukuma kan mutuwar ba tukuna, amma jam’iyyar ta bayyana marigayin a matsayin ɗan siyasa mai gaskiya da jajircewa wanda ya tsaya tsayin daka kan manufofin jam’iyya da akidunta.

A cikin ta’aziyyar da ta aika, PDP ta roki Allah ya jikansa tare da ba da hakuri ga gwamnati da al’ummar Jihar Bayelsa bisa wannan rashi mai raɗaɗi.

Ewhrudjakpo ya kasance Mataimakin Gwamna Douye Diri tun shekarar 2020 bayan zabensu na 2019, kuma an sake tabbatar da shi a matsayin mataimaki bayan nasarar su a zaben 2023.

Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa, Kafin mutuwar sa,  Lawrence Oboraw-Harievwo Ewhrudjakpo, bai halarci sanarwar sauya sheƙar Gwamna Diri zuwa APC ba, sannan ya kai ƙara kotu domin hana Majalisar Dokokin Jihar Bayelsa ƙoƙarin tsige shi saboda cigaba da kasancewarsa a PDP.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here