An kuma zargi Malami da ɗansa da ajiye makamai a gidansu da ke Gesse Phase II, Birnin Kebbi LGA, Jihar Kebbi ba tare da izini na doka ba.
DSS ta ce a cikin tuhuma ta farko, tsohon AGF ya kasance cikin shirin tallafawa ta’addanci, yayin da a tuhumar biyu zuwa biyar, Malami da ɗansa sun aikata laifi na mallakar bindiga kirari Sturm Magnum 17-0101 da harsasai 16 Redstar AAA 5’20 masu rai da harsasai 27 Redstar AAA 5’20 da aka harba, abin da ya saba wa dokar yaƙi ta’addanci (Prevention and Prohibition) Act, ta 2022 da dokar mallakar makamai ta 2004.
Malami da ɗansa sun musanta laifukan lokacin da aka karanta tuhumar a gabansu.
Bayan sun musanta, lauyan ƙara, Calistus Eze, ya roƙi kotu ta tsare su a hannun DSS har zuwa lokacin fara shari’a.
Sai dai Lauyan kariya, Shuaibu Aruwan SAN, ya roƙi a ba su belin baki, yana mai cewa an tsare su a hannun DSS fiye da makonni biyu.
Amma mai shari’a Joyce Abdulmalik ta ƙi amincewa da roƙon belin baki, ta ce kotu ce mai hurumi, ta umurci lauya ya shigar da roƙon belin baki na hukuma.
Ta kuma umurci a tsare su a hannun DSS har zuwa ranar 20 ga Fabrairu domin fara shari’a.
Solacebase








