Da yammacin yau Litinin ne ake sa ran gudanar da jana’izar Marigayi Sheikh Usman Idris Kusfa da aka fi sani da Rigi-Rigi wanda ya rasu a daren jiya Lahadi.
Surikin malamin, Malama Abubakar Ɗanyaro, ne ya tabbatar da rasuwarsa inda ya ce, za a gudanar da jana’izar marigayin a yau Litinin da misalin karfe 4:30 na yamma a garin Zaria.
Sheikh Rigi-Rigi ya yi fice da salon wa’azinsa, musamman wajen bayyana ƙaramomin waliyyai da manyan malamai.
Da fatan Allah ya gafarta masa.







