Wata gobara da ta tashi a kasuwar Singa da ta haifar da gagarumar asarar dukiya, tare da jikkata mutane da dama.
Gobarar, ta tashi ne a rukunin shagunan Mazaf, inda ta ƙone kayayyaki masu yawa da ba a kai ga tantance adadinsu ba.
Rahotonni sun bayyana cewa, gobarar ta afku ne da tsakar dare a kan titin Bello Road, cikin babbar kasuwar ta Singa.
Sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto ba a kai ga tabbatar da musabbabin tashin ta ba, yayin da hukumomi ke ci gaba da tattara bayanai.
Ɗan uwan mamallakin rukunin shagunan da abin ya shafa, Barista Junaidu Muhammad Zakari, ya bayyana cewa, wutar ta yi babbar barna.
Shugaban kasuwar Singa da kewaye, Alhaji Musa Ibrahim Nabanki, ya ce an riga an fara gudanar da bincike kan lamarin.
A nasa bangaren, jami’in hulɗa da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Saminu Yusuf Abdullahi, ya ce za su fara cikakken bincike da zarar an shawo kan sauran birbishin wutar.








