Home Labarai Gwamnatin Tarayya ta maka Elrufa’i a kotu bisa zargin yin kutse cikin...

Gwamnatin Tarayya ta maka Elrufa’i a kotu bisa zargin yin kutse cikin wayar NSA

0

Gwamnatin Tarayya ta shigar da kara mai kunshe da tuhume-tuhume uku a kan tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasiru El-Rufai, bisa zargin cewa ya yi kutse ba bisa ka’ida ba cikin wayar sadarwar Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawara kan Tsaro Nuhu Ribadu.

A cikin karar da Gwamnatin Tarayya ta shigar a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta hannun Hukumar Tsaron Farin Kaya ta Kasa DSS, an zargi tsohon gwamnan, wanda ya taba rike mukamin Ministan Babban Birnin Tarayya FCT a lokacin gwamnatin tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo, da aikata laifin tare da wasu mutane da a halin yanzu suke gudu.

Gwamnatin Tarayya ta shaida wa kotu cewa wanda ake kara ya amince da hannu a cikin lamarin a ranar 3 ga Fabrairu, lokacin da ya bayyana a matsayin bako a wani shirin a gidan talabijin na Arise.

An tuhume shi da aikata laifi karkashin sashe na 12 (1) na Dokar Hana Laifukan Internet Haramtawa, Rigakafi da sauransu wadda aka yi wa Gyara ta shekarar 2024.

A tuhuma ta biyu, an ce tsohon gwamnan, wanda yake daya daga cikin manyan mambobin kawancen ‘yan siyasa na adawa da ba su gamsu da gwamnatin Shugaban Kasa Bola Tinubu ba, yana da masaniya cewa wani ya yi kutse cikin sadarwar NSA ba bisa ka’ida ba amma bai kai rahoton laifin ga hukumomin tsaro da suka dace ba.

An kuma yi zargin cewa ta hanyar amfani da kayan aikin fasaha wajen katse kiran wayar NSA, wadanda ake kara sun jefa lafiyar jama’a da tsaron kasa cikin hadari, tare da haifar da fargaba mai ma’ana a tsakanin ‘yan Najeriya, laifin da ya saba wa sashe na 131(2) na Dokar Sadarwa ta Najeriya ta shekarar 2003.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here