Home Labarai Hisbah ta kama matasa 9 da ta ke zargi da yawon Ragaita Labarai Hisbah ta kama matasa 9 da ta ke zargi da yawon Ragaita By ahsant - December 27, 2025 0 FacebookTwitterPinterestWhatsAppCopy URL Hukumar Hisbah ta jihar Kano, ta ce, ta kama wasu matasa mata su 8 da namiji 1 bisa zargin su da yin yawon banza, a yayin wani samame da ta gudanar a wasu unguwanni da manyan tituna a fadin jihar. Mataimakin Babban Kwamandan hukumar a ɓangaren Ayyuka Dakta Mujahid Aminuddeen, ne ya tabbatar da hakan ta cikin wani saƙon murya da ya raba wa manema labarai. A cewarsa, an kama mutanen ne a yayin samamen da aka gudanar a wurare da dama da suka hada da titin zuwa Gidan Zoo, Banana Zoo Road, Ahmadu Bello Way, Lamido Crescent Way, Tukur Road Nasarawa GRA, Lodge Road Nasarawa GRA, titin zuwa Asibitin Nasarawa, Magajin Rumfa Road, Sultan Road Nasarawa GRA da kuma Audu Bako Way. Haka kuma, Dakta Mujahid Aminuddeen ya ƙara da cewa, hukumar na ci gaba da gudanar da bincike kan wadanda aka cafke, domin daukar matakin da ya dace bisa tanadin dokokin jihar.