Bishop na Cocin Katolika a Diocese na Kano, Dakta John Namaza Niyiring, ya yi bikin Kirsimeti ta hanyar kai ziyara ta ruhaniya watau pastoral visit a gidan gyaran hali da tarbiyya na Goron Dutse a Kano, inda ya gudanar da gagarumin biki tare da ɗaurarru da isar da saƙonnin fata, zaman lafiya da gafara da kuma sabuwar rayuwa.
Wannan ziyara na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Hukumar Gyaran Hali ta Ƙasa (NCoS), reshen Kano, CSC Musbahu Lawan Kofar Nassarawa, ya fitar, inda ya ce an shirya ta ne domin ɗaga ƙwarin gwiwar fursunoni a lokacin bukukuwan Kirsimeti.
A yayin bikin, Bishop Niyiring ya jaddada cewa haihuwar Annabi Isa Almasihu na nuni da sabon farawa da ceto, ya na mai tunatar da ɗaurarru cewa babu wanda aka manta da shi ko aka watsar yayin da ya ke cikin halin ƙunci.
Ya ƙarfafa musu gwiwa da su kasance masu fata, juriya da jajircewa wajen gyaran halayensu, tare da tabbatar musu da cewa Coci na ci gaba da yi musu addu’a da tallafi.
A wani bangare na ziyarar, Bishop ɗin ya ɗauki nauyin sakin ɗaurarru 11, domin su haɗu da iyalansu a lokacin Kirsimeti.
Haka kuma ya ba da gudummawar abinci, lemo, tufafi da ruwan sha domin inganta jin daɗin ɗaurarru.
Da ya ke jawabi a madadin shugaban hukumar kula da gidajen gyaran hali na Kano, ACC Kafilu Abdullahi, Jami’in da ke kula da gidan gyaran hali na Goron Dutse ya gode wa Bishop ɗin bisa ci gaba da tallafi da suke bai wa cibiyar.
“Wannan ziyara na nuna kyakkyawar haɗin kai tsakanin ƙungiyoyin addini da Hukumar Gyaran Hali ta Ƙasa,” in ji ACC Kafilu.
Ya ƙara da cewa tsoma bakin Bishop ɗin a kai a kai ya yi matuƙar tasiri a rayuwar fursunoni tsawon shekaru.
ACC Kafilu ya kuma tunatar da cewa tallafin Bishop bai tsaya ga ziyarar bukukuwa kaɗai ba, inda ya ce an ba da kwamfutoci shida a bara domin taimaka wa fursunoni su ci gaba da karatu, daidai da manufar gyara da mayar da su cikin al’umma ta Hukumar Gyaran Hali.
Solacebase








