Home Labarai Majalisa ta amince da  Mohammed da Eyesan a matsayin shugabannin NMDPRA da...

Majalisa ta amince da  Mohammed da Eyesan a matsayin shugabannin NMDPRA da NUPRC

0

Majalisar Dattawan Najeriya ta tabbatar da naɗin Saidu Mohammed da Oritsemeyiwa Eyesan a matsayin manyan shugabannin hukumomin kula da harkar man fetur na ƙasa.

Oritsemeyiwa Eyesan an tabbatar da shi a matsayin babban daraktan hukumar kula da hakar man fetur ta ƙasa NUPRC.

Haka kuma, majalisar ta tabbatar da Saidu Mohammed a matsayin babban daraktan hukumar kula da man fetur ta ɓangaren da kayyade farashi NMDPRA.

Tabbatarwar ta biyo bayan nazari da amincewa da rahoton kwamitin haɗin gwiwa na majalisar dattawa kan harkokin man fetur na ɓangaren sama, ɓangaren ƙasa da gas.

Kwamitin ne ya gudanar da tantancewa da bincike kan waɗanda aka zaɓa kafin miƙa rahotonsa ga majalisar dattawa domin yanke shawara.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya rawaito cewa majalisar dattawa ta amince da rahoton kwamitin baki ɗaya, lamarin da ya kai ga tabbatar da naɗin Mohammed da Eyesan a matsayin shugabannin hukumomin.

Solacebase

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here