Home Labarai NECO ta saki da sakamakon jarrabawar Nuwamba/Disamba ta 2025

NECO ta saki da sakamakon jarrabawar Nuwamba/Disamba ta 2025

0

Hukumar shirya jarabawar kammala Sakandare ta Najeriya NECO, ta saki sakamakon jarabawar ta Nuwamba/Disamba ta shekerar 2025, inda aka samu kashi 71.63 cikin 100 na waɗanda suka ci jarabawar.

Shugaban hukumar ta NECO Farfesa Dantani Ibrahim Wushoshi, ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da ya gudanar a Shalkwatar hukumar da ke Minna yau Talata.

Ya ce an gudanar da jarabawar daga 26 Nuwamba zuwa 13 Disamba 2025, yayin da aka kammala duba takardun daga 5 Janairu zuwa 21 Janairu 2026.

Ya bayyana cewa an saki da sakamakon ne bayan kwanaki 52 da kammala rubuta jarrabawar ƙarshe.

A cewarsa, dalibai 96,979 ne suka yi rajista domin jarabawar, ciki har da maza 51,823 da mata 45,156.

Ya kara da cewa dalibai 95,160 ne suka zauna jarabawar, inda maza 50,785 da mata 44,375 suka halarta.

Daga cikinsu, dalibai 93,425 ne suka rubuta harshen Ingilishi, kuma 73,167 daga ciki sun samu kiredit da dama, wanda ke wakiltar kashi 78.32 cikin 100.

A fannin lissafi kuma, dalibai 93,330 ne suka zauna jarabawar, inda 85,256 suka samu kiredit da dama, wato kashi 91.35 cikin 100.

Jimillar dalibai 68,166 sun samu kiredit biyar da sama da hakan ciki har da Ingilishi da lissafi, yayin da 82,082 suka samu kiredit biyar da sama da biyar ba tare da la’akari da Ingilishi da lissafi ba.

Farfesa Ibrahim-Wushishi, ya bayyana cewa jarabawar SSCE mai zaman kanta na bai wa dalibai wata dama ta biyu wajen neman guraben karatu a jami’o’i da sauran manyan makarantu a ciki da wajen Najeriya.

Ya kara da cewa jarabawar ta kunshi fannoni 16, kuma fitar da sakamakon wani muhimmin mataki ne na cika kudurin NECO na gudanar da sahihiyar jarabawa.

Ya kuma bayyana cewa an kama dalibai 9,016 da laifuffukan satar jarabawa iri-iri, adadin da ya fi na 2024 da kashi 31.7 cikin 100.

Haka kuma, an ba da shawarar haramta wa masu sa ido biyar aikin jarabawar bisa taimakawa wajen satar jarabawa, inda biyu daga ciki suka kasance ƴan birnin tarayya Abuja sai ɗaya-ɗaya daga Kano da Adamawa da Ondo.

An kuma ba da shawarar cire cibiyoyin jarabawa hudu daga jerin masu gudanarwa saboda satar jarabawa baki ɗaya, ciki har da cibiyoyi daga Niger, Yobe da Kano.

Solacebase

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here