Jami’an ƴan sanda sun sanar da cafke wata matar aure mai shekaru 18 a garin Potiskum na jihar Yobe, wadda aka sakaye sunanta bisa zarginta da yanke al’aurar mijinta.
Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar ta Yobe, SP Dungus Abdulkarim, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Damaturu, inda ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 1 na dare ranar 6 ga Fabrairu.
Sanarwar ta nuna cewa an kai rahoton lamarin ofishin ’yan sandan Potiskum da misalin karfe 3 na rana a ranar da lamarin ya faru, bayan matar ta tsere daga wurin da aka aikata laifin.
Rundunar ’yan sandan ta ce matar, wadda ke tsere a halin yanzu, ta yi amfani da wuka mai kaifi wajen raunata mijinta kafin ta gudu, lamarin da ya jawo sanadiyyar yi masa mummunan rauni.
Bayan samun rahoton, jami’an ’yan sanda sun garzaya wurin tare da kai mutumin zuwa asibitin kwararru na jihar Yobe da ke Potiskum domin samun agajin gaggawa, daga nan aka tura shi zuwa cibiyar kula da lafiya ta tarayya da ke Azare inda yake samun kulawa.
Rundunar ta ce bincike na ci gaba domin cafke wadda ake zargi da kuma gano ainihin abin da ya jawo aikata laifin, tare da bayyana cewa ba za a fitar da wasu muhimman bayanai ba domin kare mutumin daga ƙarin raɗaɗi.
Kwamishinan ’yan sandan jihar Yobe, Emmanuel Ado, ya yi Allah wadai da wannan ɗanyen aiki, inda ya bayyana cewa, ya kamata aure ya kasance bisa girmamawa da fahimta da hakuri, ba tare da tashin hankali ko cin zarafi ba.








