Gwamnatin tarayyar Najeriya ta sanar da shirinra na gudanar da taron Majalisar tattalin arzikin ƙasa a ranar Litinin domin ƙarfafa daidaiton harkokin tattalin arziki da kuma bunƙasar ci gaba mai haɗa kowa a dukkan jihohi.
Mai taimaka wa shugaban ƙasa na musamman kan kafafen yaɗa labarai da sadarwa a ofishin mataimakin shugaban ƙasa, Stanley Nkwocha, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Lahadi.
Nkwocha ya ce gwamnonin jihohi talatin da shida tare da manyan masu ruwa da tsaki na ƙasa za su halarci taron daga ranar tara zuwa goma ga watan Fabrairu a dakin liyafa na fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
Ya ƙara da cewa mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima, wanda ke shugabantar Majalisar tattalin arzikin ƙasa, zai jagoranci taron na kwanaki biyu, inda za a tattauna batutuwan da suka shafi daidaita harkokin kuɗi, tara jari da kuma dabarun ci gaba na bai ɗaya tsakanin gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi.
Haka kuma ya bayyana cewa shugaban ƙasa Bola Tinubu zai halarci taron a matsayin baƙon girmamawa na musamman, yayin da ake sa ran manyan jami’an gwamnati, abokan hulɗar ci gaba da shugabannin ɓangaren masu zaman kansu za su halarta.
Haka kuma, ya ƙara da cewa ministan kasafi da tsare-tsaren tattalin arziki, Sanata Abubakar Bagudu, ne ya shirya taron, inda ake sa ran zai samar da muhimman manufofin da jihohi za su bi domin daidaita kansu da ajandar tattalin arziki ta dogon lokaci ta gwamnatin tarayya.
Babbar Sakatariya a ma’aikatar kasafi da tsare-tsaren tattalin arziki ta tarayya kuma sakatariyar Majalisar tattalin arzikin ƙasa, Dakta Deborah Odo, ta bayyana cewa taron zai mayar da hankali kan manyan batutuwan tattalin arziki na ƙasa domin ƙarfafa bunƙasar tattalin arziki da ci gaba a faɗin ƙasar.
Solacebase








