Majalisar Wakilai ta zargi bankunan kasuwanci da aikata ba daidai ba ta hanyar cire kuɗaɗe daga asusun kwastomomi ba tare da tura su inda ya dace ba.
Wannan zargi ya fito ne yayin wani zama na bincike da kwamitin wucin gadi na Majalisar ya gudanar a Abuja.
Shugaban kwamitin, wanda Rep. Kelechi Nwogu, ya wakilta yace wajibi ne duk wani caji ko cire kuɗi da bankuna ke yi a asusun kwastomomi ya kasance bisa ka’ida,sannan a yi amfani da shi ta hanyar da ta dace.
Ya ce za su kare ’yan Najeriya daga cirar kudaden da ake yi musu ba tare da ka’ida ba wanda kuma hakan ke cutar da su.
Kwamitin ya bayyana cewa an gayyaci Ma’aikatar Kuɗi ta Tarayya, kuma za su haɗa gwiwa da Ofishin Akanta Janar na Tarayya da kuma hukumar hana cin hanci da rashawa (EFCC) tare da bankunan kasuwanci wajen gudanar da cikakken bincike kan batun.








