Gwamnatin jihar Neja ta mika yara 100 da aka ceto, wadanda aka sace daga Makarantar Katolika ta St Mary’s da ke Papiri ga iyayensu bayan makonni biyu a hannun waɗanda suka sace su.
Harabar makarantar ta cika da iyaye, waɗanda ke cikin murna da kuma fargaba yayin da suke jiran ganin ’ya’yansu da aka kuɓutar, a lokacin da aka tafi da yaran gida daga Minna, babban birnin jihar.
Kwamishinan ’yan sanda ya bayyana cewa an duba lafiyar yaran, kuma dukkansu suna cikin koshin lafiya
Iyayen da suka kwana suna jiran wannan rana sun bayyana cewa ganin ’ya’yansu cikin koshin lafiya ya kasance babban abin farin ciki a gare su.
Gwamnatin jihar ta tabbatar da cewa tana ci gaba da aiki tukuru domin ganin an sako sauran dalibai 153 da ma’aikata 12 waɗanda har yanzu suke hannun ƴan bindiga.
Gwamnatin ƙasar ta yi alkawarin karfafa tsaro a makarantu domin hana faruwar irin wannan hari a nan gaba.








