Home Labarai Sokoto: Sojoji sun kashe jagoran yan bindiga Kachalla Kallamu

Sokoto: Sojoji sun kashe jagoran yan bindiga Kachalla Kallamu

0

Dakarun Rundunar Bataliya ta 8 ta Sojin Najeriya sun kashe shahararren jagoran ’yan bindiga, Kachalla Kallamu, a ƙaramar hukumar Sabon Birni ta jihar Sokoto kamar yadda Wata majiyar jami’an tsaro ce, ta bayyana wa labarai hakan da safiyar yau Laraba.

Majiyar ta ce Kallamu, wanda shakiki ne ga shahararren jagoran ’yan bindiga, Bello Turji, an kashe shi ne tare da haɗin gwiwar ’yan sa-kai a yankin, a wani samame na musamman da sojojin Nigeria Army suka gudanar a ƙauyen Karawa da safiyar ranar Litinin.

Rahoton ya kara da cewa Kallamu, wanda ya fito daga Garin-Idi a Sabon Birni, ya jima yana addabar al’ummomin yankin, kuma kwanan nan ya dawo daga jihar Kogi bayan ya gudu sakamakon farmakin sojoji a watan Yuni 2025, inda aka ce ya nemi mafaka.

Mai ba Gwamnan Jihar shawar kan tsaro kanal Ahmad Usman mai ritaya, da wasu mazauna jihar sun yabawa Sojojin Najeriya kan nasarorin da suka samu a yaki da ’yan bindiga.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here