Home Tsaro Rundunar Kishin Kano ta sha, alwashin yaƙi da ayyukan Daba

Rundunar Kishin Kano ta sha, alwashin yaƙi da ayyukan Daba

0

Rundunar Kishin Jihar Kano ta jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki tukuru domin ganin an kawo ƙarshen fadace-fadacen daba, tare da taimakawa wajen rage matsalar rashin aikin yi a tsakanin matasa.

Kungiyar ta bayyana hakan ne a dai-dai lokacin da ta ke shirin cika shekaru biyu da kafuwa.

Shugaban kungiyar, Manjo Janar Ibrahim Sani, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da rundunar ta shirya a Kano.

Manjo Janar Ibrahim Sani, ya ce, sun yi haɗin gwiwa da Hukumar Yaki da Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa, reshen Jihar Kano, domin yaƙi da wannan mummunar dabi’a da ke addabar matasa da al’umma baki ɗaya.

Ya ƙara da cewa rundunar za ta ci gaba da tallafawa fannin ilimi ta hanyar samar da kayan koyo da koyarwa a makarantun firamare da sakandare, tare da haɗin gwiwa da Gidauniyar Hasnif.

Haka kuma ya ce za su rika kai magunguna da kayan kimiyya da fasaha zuwa makarantu domin inganta koyarwa da lafiyar ɗalibai.

Rundunar ta bayyana ƙwarin gwiwarta na ci gaba da aiki tare da gwamnati da al’umma domin samar da zaman lafiya da ci gaban jihar Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here