Rundunar ƴan sandan Jihar Kano ta ce, ta cafke mutane uku da ake zargin su da hannu a kisan gillan da aka yi wa wata uwar gida da ’ya’yanta shida a unguwar Dorayi Chiranchi da ke cikin birnin Kano.
Rundunar ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawunta CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar a yau Lahadi, inda ya bayyana matakan tsaro da aka ɗauka domin dakile laifuka masu tsanani a jihar.
Rundunar ta ce, kama mutanen 3 ya biyo bayan wani shiri na bayanan sirri da Sufeton ƴan sandan ƙasa, Kayode Adeolu Egbetokun, ya bayar da umarni a kansa, tare da jagorancin Kwamishinan ƴan sandan Jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori.
An aiwatar da Kamen ne ta hannun ƙwararru a fannin bincike da haɗin gwiwar makwabta tsakanin ƙarfe 10:00 na dare a ranar 17 ga Janairu zuwa ƙarfe 4:00 na Asuba.
Rundunar ƴan sandan ta bayyana sunayen mutanen da aka cafke da suka haɗa da Umar Auwalu mai shekaru 23 daga unguwar Sabuwar Gandu, Isyaku Yakubu wanda aka fi sani da Chebe mai shekaru 40 daga unguwar Sagagi, da Yakubu Abdulaziz wanda aka fi sani da Wawo mai shekaru 21 daga unguwar Sabon Gida Sharada, dukkansu a Kano.
Umar Auwalu, wanda ɗan’uwan matar da aka kashe ne, ya kasance jagoran ƙungiyar masu aikata laifin, inda bincike ya nuna shi ne ya tsara kisan, tare da danganta ƙungiyar da wasu hare-haren tashin hankali a Kano, ciki har da kisan wasu mata biyu da kona su a unguwar Tudun Yola.
Kayayyakin da aka gano daga hannun mutanen sun haɗa da tufafi huɗu masu jini, wayoyin hannu biyu na mamatan, adda, gora, kuɗaɗen da ake zargin an sace daga wurin, da wasu makamai masu haɗari, yayin da bincike ke ci gaba domin gano cikakken girman ayyukan ƙungiyar.
Rundunar ƴan sandan Jihar Kano ta tabbatar wa al’ummar jihar kudirinta na ganin an gurfanar da duk masu hannu a aikata laifuka gaban shari’a domin tabbatar da adalci da tsaron rayuka da dukiyoyi.
Samun wannan nasara ta ƴan sanda dai na zuwa ne sa’o’i kaɗan bayan da Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya nuna matuƙar alhininsa bisa kisan gillar tare da bayyana lamarin a matsayin tsantsar rashin imani.
Gwamnan ya bayyana hakan ne ta hannun mai magana da yawunsa, Sunusi Bature Dawakin Tofa, inda gwamnan ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan, al’ummar Dorayi Chiranchi da kuma daukacin jama’ar jihar Kano, tare da yin addu’ar Allah Ya gafarta wa mamatan Ya kuma ba iyalansu juriyar jure wannan babban rashi.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa kisan uwa da ’ya’yanta nata abu ne da ba za a taɓa amincewa da shi ba, tare da cewa gwamnatinsa ba za ta bari irin wannan mummunan laifi ya wuce ba tare da hukunci ba.
Gwamnan ya kuma bayar da umarnin gaggawa ga rundunar ’yan sandan jihar Kano da su bazama farautar masu aikata laifin tare da tabbatar da cafke su da gurfanar da su gaban shari’a, yana mai gargadin cewa duk wanda aka samu da hannu a ciki zai fuskanci hukuncin doka ba tare da sassauci ba.








