Home Labarai Bauchi: Ƴan sanda sun kama mutane 6 bisa zargin su da yin...

Bauchi: Ƴan sanda sun kama mutane 6 bisa zargin su da yin fashi

0

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi ta cafke mutane shida bisa zargin haɗa kai da aikata fashi da makami a Karamar Hukumar Giade, tare da kwato babura da wasu kayayyakin da ake zargin na sata ne.

Rundunar ta ce cafke mutanen ya biyo bayan samun sahihan bayanan sirri kan ayyukan masu laifin a yankin.

Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi, SP Nafiu Habib, be ya bayyana hakan ya na mai bayyana cewa fashin ya shafi Mohammed Musa da Auwal Maidawa, inda wasu mutane dauke da adduna, wukake, sanda da bindigar gargajiya suka kai musu hari suka jikkata su tare da kwace musu kayayyaki.

Baturen ’Yan Sanda na Giade, CSP Bello Yusuf Kumo, ne ya jagoranci jami’an da suka cafke Aminu Abdulkadir mai shekaru 22, wanda daga bisani ya fallasa sauran da ake zargi ciki har da Habu Musa, Adamu Samaila da Yusuf Sabo, dukkansu mazauna Giade.

Rundunar ta ce binciken farko ya nuna mutanen suna addabar garin Giade ta hanyar shiga gidaje da kwace wayoyi, kayan sawa da wasu na’urori, inda darajar kayan da aka sace ta kai kimanin naira miliyan 1 da dubu dari biyu.

An kuma kwato babura guda biyu, wukake masu kaifi, kayan fasa gida, katunan ATM da wasu kayayyaki, yayin da rundunar ta ce tana ci gaba da bincike kafin gurfanar da wadanda ake zargi a gaban kotu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here