Home Labarai Jami’an DSS sun kama Abubakar Malami bayan fitowarsa daga gidan yarin Kuje

Jami’an DSS sun kama Abubakar Malami bayan fitowarsa daga gidan yarin Kuje

0

Hukumar tsaron farin kaya ta ƙasa DSS ta kama tsohon Antoni Janar na Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami SAN, a ranar Litinin jim kaɗan bayan fitowarsa daga Gidan Gyaran Hali na Kuje da ke Abuja.

Jami’an Hukumar Tsaron Farin Kaya ta Ƙasa DSS sun ɗauke shi ne nan take bayan ya kammala ficewa daga harabar gidan gyaran halin, inda aka shiga da shi cikin motar jami’an tsaro ba tare da bata lokaci ba.

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Ƙasa EFCC ta fayyace cewa ba ita ce ta sake kama Malami ba bayan fitowarsa daga gidan yari, tana mai cewa ba ta da hannu a ɗaukar matakin da aka gani.

Hukumar Gidajen Gyaran Hali ta Ƙasa ta tabbatar da cewa an saki Malami ne bayan ya cika dukkan sharuddan belin da kotu ta gindaya masa, tare da kammala dukkan matakan da ake buƙata kafin sakin sa.

Bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta ya nuna yadda ake jagorantar Malami zuwa wata bakar mota ƙirar Toyota Hilux bayan fitowarsa daga gidan gyaran halin, lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce a tsakanin jama’a.

Sakin Malami ya biyo bayan bayar da belinsa a ranar 7 ga watan Janairu ta hannun Mai Shari’a Emeka Nwite na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, inda kotun ta amince da belin Malami da matarsa da ɗansa kan kuɗin N500m kowannensu tare da tsauraran sharuɗɗa, ciki har da miƙa fasfo ɗin tafiye-tafiye da hana fita ƙasar waje ba tare da izini ba.

Hukumar EFCC ta gurfanar da Malami, matarsa Asabe da ɗansu a gaban kotu bisa tuhume-tuhume 16 da suka shafi wanke kuɗi kimanin N8.7bn, inda ake zargin sun yi amfani da kamfanoni, asusun banki da sayen kadarorin alfarma domin ɓoye kuɗaɗen da ake zargin an samo ta haramtacciyar hanya.

Solacebase

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here