Home Labarai An ga jinjirin watan Ramadan a ƙasar Saudiyya

An ga jinjirin watan Ramadan a ƙasar Saudiyya

0

Rahotonni daga ƙasar Saudi Arabia, sun tabbatar da cewa an ga jinjirin watan Ramadan, lamarin da ke nuna cewa lokaci ya yi da Musulunci za su fara gudanar da Azumin watan mai alfarma.

A cewar hukumar kula da masallatai masu alfarma na ƙasar, mahukuntan ƙasar za su ayyana ranar Laraba 18 ga Fabrairu a matsayin ranar farko ta watan Ramadan.

Tun da farko an sanar cewa za a gudanar da duban jinjirin watan a Hawtat Sudair da kuma Tumair a gundumar Al-Majma’ah.

Abdulaziz Al-Muainaa daga cibiyar lura da wata ta Al Hareeq ya ce, “Rana za ta fāɗi dai-dai ƙarfe 5:52 na yamma a agogon ƙasar, kuma yanayin sararin samaniya ya dace domin ganin jinjirin watan na Ramadan.”

Da ta ke sanar da ganin jinjirin watan a ranar Talata, hukumar ta ce, “An ga jinjirin watan a Saudiyya, Saboda haka, watan Ramadan na shekarar 1447 zai fara daga daren yau Talata.

A halin yanzu, Musulmi a Najeriya za su jira sanarwa kan fara Ramadan daga Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma Amirul Muminina, Muhammad Sa’ad Abubakar na uku.

Watan Ramadan dai, shi ne wata na tara a Kalandar Musulunci kuma mafi tsarki a shekara.

Ana tunawa da saukar da Alƙur’ani ga Annabi Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi a cikin watan, wanda kuma ake dacewa da Lailatul Qadri, wadda ake yi a cikin kwanaki goma na ƙarshe na watan Ramadan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here